Tukwici da dabarun samun lafiyan Jiki: Idan ka na da miki, ka kauce wa waɗanan abinci guda biyar

Tukwici da dabarun samun lafiyan Jiki: Idan ka na da miki, ka kauce wa waɗanan abinci guda biyar

 

Kana fama da ciwon Miki? Ka kauce wa waɗanan abinci.

Mutane da yawa suna da ciwon miki, idan ba a kula da shi ba, zai zama mugun ciwo. Ciwon miki ya kan faru idan mutum ya samu gyambo ko rauni cikin tumbinsa. Wannan yana faruwa idan gamsai mai kauri, wanda ya kamata ya kare tumbi, ya rage sossai. Sai ruwan da ke narke abinci zai kama cinye tumbi.

Ciwon miki yana da magani idan ka ɗauki mataki cikin lokaci. Za ka ɗauki matakai kamar na magani, yanayin rayuwa, da kuma kiyayewa da sauran aububuwan da ke ƙara tsananin ciwon miki.

Ga abincin da za ku kauce wa domin samun warke daga ciwon miki.

1. Abinci mai yaji: Abinci mai yaji yana ƙara tsananin ciwon miki. Idan ka ci abinci mai yaji, yajin zai taɓa raunin da yake cikin tunbi.

2. Shayin Kofi: Shayin kofi ba zai kawo ciwon miki ba. Amma, kofi yana wanke ciki sossai. Idan kana da miki, ya kamata ka bar shan shayin kofi domin zai ƙara fadin raunin ciki. Wannan zai hana warkewan ciwon miki.

3. Barasa ko giya: Idan kana da ciwon miki, giya ko barasa zai ƙara ruwan yacid na tumbi. Wannan zai ƙara matsalar miki, kuma ciwon ba zai sake warkewa ba.

4. Jan Nama (Kamar Naman Shanu): Duk wanda yake da cûtar miki zai ƙokarta ya bar cin jan nama. Jan nama yana kara yawan ruwan yacid cikin tumbin mutum. Wanna shine domin jan nama ba ya saurin narkewa. Gara mai ciwon miki ya ci naman kaza, talo-talo, da sauran nama masu saurin narkewa cikin tumbi.

5. Abinci fakiti: Idan kana fama da ciwon miki, ya kamata ka rabu da cin abinci kamar indomie, taliya, gurasa(waton burodi), da sauran abincin da aka yi a kamfani. Ka saba da cin abinci kamar ganye, ʼƴaʼƴan itace da kuma ruwa masu yawa.

Idan mai ciwon miki ya lura da waɗanan kaʼidoji, zai samu sauƙi, kuma zai warke cikin lokaci.  

Punky

Cool Minded Blogger and Webmaster +2348022050583

Leave a Reply

Your email address will not be published.

%d bloggers like this: