Sanusi Lamido Sanusi: Án yi bikin Kamu naʼƳar Sarkin Kano, gaba da shirin Bikin Aure

Sanusi Lamido Sanusi: Án yi bikin Kamu naʼƳar Sarkin Kano, gaba da shirin Bikin Aure

 

Zá a yi bikin aure na Sarkin Kano a ranar 23 ga watan Disamba, cikin wannan shekara na 2016.

A cikin wannan mako, za a yi bikin ɗaurin aure tsakánin Fulani Siddika da Malam Abubakar Umar Kurfi. Domin shirya ma wannan babbar rana, an yi ma Gimbiya bikin Kamu a fadan Sarki a ranar 18 ga watan Disamba.

 

Bikin Kamun Amarya, ɗaya ne daga tsohon alʼada na auren Hausawa da Fulbe. Kamar yanda ake wannan alʼada, Dangi Ango da iyalinsa za su nemi shawarwari domin a fito da Amarya tare da abokanin ta. Wannan tsari yana ɗaukan lokaci kusan minti talatin (30) kafin a shiga nishadin bikin liyafar Amarya.

 

A ranar bikin Kamin Amarya, Fulani Siddika ta shiga wani tunani domin zafin rabuwa da abokanin wargi. Ta fashe da kuka a ranar biki, kuma ƙaninta ya baza vidiyo na kuka akan shafinsa na Twitter akan yanar gizo-gizo da sauran naʼurorin yanar gizo-gizo.

 

Bayan an kammala bikin Kamu, za a yi bikin aure wanda zai kasance a fadar Sarkin Kano (Emir Sanusi Lamidio Sanusi).

Za ku tuna da cewa an yi bikin ɗaurin aure na ʼƴar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, waton bikin auren Zahra, a makon da ya wuce. Zahra ta auri Ahmed Indimi a garin Abuja.

 

Bugu da ƙari, akwai labari cêwa za a yi bikin aure na Stephanie Coker da Daniel Aderinokun a kwanan gaba.

ʼƳan Gidan jaridan Pulse NG masu kawo muku labarai na aure, suna yi ma maʼaurata fatar Alheri, albarka na Allah (SWA) da kuma aure mai daɗin zuma. Amin.

Punky

Cool Minded Blogger and Webmaster +2348022050583

Leave a Reply

Your email address will not be published.

%d bloggers like this: