Mansur Ɗan Ali: Ministan Tsaro ya kai ma Shugaban Ƙasar Tchadi ziyara

Mansur Ɗan Ali: Ministan Tsaro ya kai ma Shugaban Ƙasar Tchadi ziyara

Ministan Tsaro ya kai ma Shugaban Ƙasar Tchadi ziyara

Ministan Tsaro na Najeriya, Mansur Ɗan Ali, ya kai ziyara wajen Shugaban Ƙasar Tchadi (Idris Deby).

Ministan Tsaro, Mansur Ɗan Ali, ya roƙi Shugaban Ƙasar Tchadi (Idris Deby) cewa ya kira waɗanda suka yi alƙawarin taimakawa da kuɗi domin gyaran tafkin Tchadi, su cika alƙawarin su.

Deby shi ne Shugaban Gwamnatin ɗinki Afrika. Maʼaikacin Hukumar Tsaro sun saki kalamai cêwa Ministan Tsaro ya yi jagoranci zuwa Tchadi wajen Deby tare da tawagar minisitoci, da shuagabanin Tsaro, da kuma sojojin ƙasashe masu haɗin-kai wajen yaƙin Boko Haram. Ƙasashe masu fama da matsalar Boko Haram sune;Najeriya, Nijar, Kamaru da kuma Benin.

Ministan Tsaro, tare da shuagabanin hukumar tsaro, sun halarta a garin NʼDjamena domin taron tattaunawa na maʼaikatan hukuma mai kula da tafkin Tchadi.

Kakakin Ministan Tsaro, Kanar Tukur Gusau, ya ba da kalamai a ranar laraba, a lokacin da yake hira da ƴan jarida a garin Abuja.

Dan-Ali ya cê wannan kira ya zama wajibi domin a taimake sojojin tariyya na ƙasashe biyar masu yaƙi da Boko Haram. Ya roƙi shuagabanin ƙasashen Afrika su kyautata rayuwar ʼƴan ƙasan su, domin hana ʼƴan taʼadda daga aukar matasa ga mumunar ayyuka.

Da yake amsawa, Deby ya tabbatar ma baƙi cêwa shuagabanin ƙasashe masu alaƙa da ƙungiya mai kula da tafkin Tchadi, zasu bada goyon bayansu wajen tallafa ayyukan sojoji. Deby ya yi bayani cêwa zai ƙara tattaunawa da masu gudunmawa domin cika alƙawarin da suka bayar.

Shugaban Ƙasar Tchadi, ya yaba ma sojoji masu haɗin kai domin koƙarin su ga aikin share ʼƴan Boko Haram . Ya ba da umarni na cika wannan aiki cikin lokaci.

Punky

Cool Minded Blogger and Webmaster +2348022050583

Leave a Reply

Your email address will not be published.

%d bloggers like this: