Magu, Babachir Lawal: Shugaban Ƙasa Buhari ya bada umarni na bincikar Shugaban EFCC da Sakatare na Gwamnatin Tarayya

Magu, Babachir Lawal: Shugaban Ƙasa Buhari ya bada umarni na bincikar Shugaban EFCC da Sakatare na Gwamnatin Tarayya

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari

Ƴan Majalisar Dattijai sun yi zargin Sakateren Gwamnatin Tarayya da laifin almubazzaranci na ƙuɗin kwangila wanda bai aikata ba. Haka ma hukumar DSS ta zarga Shugaban EFCC, Magu.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya umurce Ministan Shariʼah, Mallam Abubakar Malami, domin ya bincike manyan maʼaikacin gwamnati wanda aka zarga da laifin cin hanci da rashawa

Kakakin
Shugaban Ƙasa, Garba Shehu, ya bayyana wannan a kalamai wanda ya yi a ranar
Lahadi, 18 ga watan Disamba.

"An jawo
hankalin Shugaban Ƙasa game da rahotanni da dama akan jaridu, wanda ya shafi
zargi na cin hanci da reshewa, wanda aka yi ma babban maʼaikata masu aiki tare
da gwamnatin Buhari".

"Game da wannan
bayani, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya umurce Ministan Shariʼah (waton
Babban Mai Shariʼah) ya bincika duk maʼaikacin gwamnati wanda ake zargi da
laifi. Idan an kama su da laifi, ba za su guji laʼanta ba".

An
zargi Sakataren Gwamnatin Tarayya (Babachir Lawal) da Shugaban Hukumar EFCC
(Ibrahim Magu) da laifin cin hanci da reshewa. Amma cikin kalamansa, Shehu bai
ambaci sunan kowa ba.

Bayan
sun yi binicike-bincike, ƴan Majalisar Dattijai sun zargi Lawal da laifin
almubazzaranci na kuɗin kwangila wanda bai aikata ba a Arewa na Gabas, a yayin
da ya yi amfani da kamfaninsa wajen nemen kwangila.

Ko
da yake, Lawal ya ƙaryata waɗanan zargin da aka yi masa, Majalisar Dattijai sun
shawarce shi ya yi murabus. Suna neman a laʼanta shi.

Haka
kuma, a ranar 15 ga watan Disamba, ƴan majalisar sun ƙi amincewa biyan buƙatan
Buhari domin tabbatar da Ibrahim Magu a mukamin Shugaban Hukumar mai kula da
cin hanci da reshewa, bayan Hukuma mai Tsaro (waton DSS) sun kawo rahoto wanda
ya zarge shi da laifuffuka.

Punky

Cool Minded Blogger and Webmaster +2348022050583

Leave a Reply

Your email address will not be published.

%d bloggers like this: