Lissafin Labarai na Pulse 2016: Ƴan wasan Kwaikwayo goma a saman teburin Kannywood na 2016

Lissafin Labarai na Pulse 2016: Ƴan wasan Kwaikwayo goma a saman teburin Kannywood na 2016

Waɗanan ƴan fasaha sun fi burge masu kallo da wasanninsu.

Ƴan wasan kwaikwayo da dama sun nuna gwaninta wanda ba zaʼa manta ba da wuri domin wasannin da suka yi. Sun ƙokarta domin yin fim masu kyau a cikin harshen Hausa, waton Kannywood.

Da ake batun
tara tsarin sunaye, Ƴan Jaridan Pulse masu kula da wasan kwaikwayo, sun yi
haɗin-kai da masanaʼata masu gwaninta a Kannywood domin yin muhawara akan
waɗanda sun cacanci fitarwa da kuma waɗanda an aminta da su domin
 fasahansu da aikinsu a cikin shekaran 2016.

Ga sunayen
manyan yan wasan kwaikwayo guda goma masu samarda wasanni wanda ya kamata ku
sani. (An rubuta sunaye ba tare da tsari akan iyawa ko wani abu daban):

Adam Zango

 

A cikin watan
Oktoba na shekaran 2016, Ɗan wasan kwaikwayo Adamu Zango ya yi sanarwa akan
shafinsa na Instagram cêwa ya fita daga Kannywood.

Ya fito a
cikin: "Basaja Gidan Yari", "Afri".

Ado Gwanja

Ya fito a
cikin: "Ɗan Kuka",
"Daga Murna".

Aisha
Aliyu Tsamiya

 

Aisha Aliyu
Tsamiya ta fara aikin kwaikwayo a shekara huɗu na baya. Ta zama tauraron wasa
bayan ta fito cikin fim mai suna "SO"
tare da Adamu Zango. Ta fita
cikin fim "Ɗakin Amarya".

Ali Nuhu

 

An san shi da
suna: Sarkin Kannywood. Ali Nuhu yana wasan Nollywood (waton wasan kwaikwayo na
harshen turanci). Ali Nuhu Darekta ne, Ɗan Wasa ne, kuma yana harhada finafinai.

Ya fito a
cikin:"Kasata", "Indon
Ƙauye"
, "Kisan Hutu".

Fati
Shuʼuma

 

Fati
Abubakar, wadda aka fi sani da suna Fati Shuʼuma, sabon tauraro ce a Kannywood.
Tana da shekaru 22.

Ta fito a
cikin: "Basma",
 "Ƴan Gambia", "Ƴar Mallam".

Jamila
Umar Nagudu

 

Ana yawan
kiranta Sarauniya Kannywood. Jamila ta fito a cikin: "Mahauciya", "Ƙaddara
Ko Son Zuciya", "Maula".

Rahama
Sadau

 

Rahama Sadau
ta shiga Kannywood a shekara na 2013. Ta zama shaharrara bayan ta taka rawa a
wani fim mai suna "Gani Ga
Wane"
Ta fito tare da
shaharraren ɗan wasa Ali Nuhu.

A watan
Oktoba na 2019, Ƙungiyar Masu Wasan Kwaikwayo sun dakatar da Rahama daga
Kannywood domin fitan da ta yi a wani waƙan soyayya tare da ClissiQ, wani
mawaƙa mai zama a garin Jos.

Ta fito a
cikin: "Ana Wata Ga Wata",
"Hallacci"

Sadiq Sani
Sadiq

 

Sadiq Sani
Sadiq ya shiga Kannywood a matsayin mai harhada wasa. Daga baya sai Sani ya
koma Ɗan Wasa.

Ya fito a
cikin: "Ƙasata",
"Iyalina"

Suleiman
Bosho

Ya fito a
cikin: "Police", "Headmaster"

Punky

Cool Minded Blogger and Webmaster +2348022050583

Leave a Reply

Your email address will not be published.

%d bloggers like this: