Jihar Lagos: Maʼaikatan Kwastan sun gane buhuhuwa ɗari da biyu na Shinkafan robobi

Jihar Lagos: Maʼaikatan Kwastan sun gane buhuhuwa ɗari da biyu na Shinkafan robobi

Maʼaikatan Kwastan sun gane buhuhuwa ɗari da biyu na Shinkafan robobi

Shugaban Kwastan na yankin Lagos ya yi wannan ƙwaƙƙafi a lokacin da yake hira da ƴan jarida a ranar Talata.

Maʼaikatan Kwastan na Yankin Ikeja, Jihar Lagos, sun kama buhun shinkafan robobi guda ɗari da biyu. Án yi akayi na wannan shinkafa da suna "Beat Tomato Rice". Ba a rubuta masa kwanan watan fitowa.

Shugaban Kwastan, Muhammad Haruna, ya yi wannan ƙwaƙƙafi a lokacin da yake hira da ƴan jaridan Hukumar Labarai na Najeriya a jihar Lagos.

Ya yi bayani cêwa án adana wannan shinkafa domin raba wa Jamaʼa kyauta a cikin lokacin biki na Kirisimati. Haruna ya ce an kama wanda ake zargi da wannan aiki a ranar Litinin. Ya yi bayani haka:

"Mun yi zaci cêwa wannan labari jita-jita ne kawai. Amma wannan kamun ya nuna cêwa lallai akwai wannan shinkafa cikin Ƙasar Najeriya."

"Mun gabatár da binciké akán wannan shinkafa. Bayan mun dafa wannan shinkafa, sai ya koma kamar danƙo. Allah dai ya san abinda zai faru da mu idan mun cinye shi"

"Muna son mu shawarci masu amfani da lokacin biki domin aikatawa wannan ayuka céwa su bar harka mai kare doka."

"Yankin Kwastan na Jihar Lagos sun ɗauki matakai na tabattar da cewa masu wannan harka sun yi hasarar kuɗin su." Ƴan jaridar NAN sun yi wannan rahoto.

Muhammad Haruna ya bayyana cêwa harkan sumogu yana faruwa a kowane ƙasa a duniya, kuma yana da wuya a dakatar da masu aikata wannan aiki. Amma ya yi waʼadi cêwa  yan hukuma suna ƙokartawa domin rage wannan matsala zuwa mafi qaranci.

Haruna ya yaba ma ƴan Najeriya waɗanda sun yi tanadi wajen  sanar da maʼaikatan kwastan wanda ya sa aka gane wannan shinkafan robobi.

Shugaban Kwastan ya umurce ƴan jarida da masu labarai cêwa su taimaka wajen ilmantar da Jamaʼa game da kasancewar wannan shinkafa na roba. Ya ce wannan labari ba jita-jita ba.

Haruna ya yi tabbacin cewa maʼaikatan Kwastan sun gane asalin kafofi na rarraba wannan shinkafa, kuma sun katange shi a nan take. Ya ce har yanzu, maʼaikatan kwastan suna bincike-bincike akan wannan matsala.

Shugaban Kwastan ya ce za su miƙa wannan Shinkafa zuwa ga Hukuma mai kula da abinci, ƙwayoyi da magunguna (waton NAFDAC) domin ƙarin bincika.

Punky

Cool Minded Blogger and Webmaster +2348022050583

Leave a Reply

Your email address will not be published.

%d bloggers like this: