Buhari: Shugaban ƙasa zai dakantar da Ministoci goma a shekara na 2017

Buhari: Shugaban ƙasa zai dakantar da Ministoci goma a shekara na 2017

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

An kawo rahoto cêwa an tattara sunayen Ministoci guda goma wanda za a dakantar da su domin rashin cika aiki.

Akwai labari cêwa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai kori Ministoci guda goma a cikin shekara na 2017.

A cikin wani rahoto na mussaman wanda ƴan gidan jarida na Thisday sun kawo, an tabattar da wannan mataki bayan Shugaban Ƙasa ya rubuta wasiƙa zuwa Majalisar Dattijai domin sanar da su game da niyyansa na maye gurbin Ministoci goma daga cikin hukumomin gwamnati.

Rahoton ya nuna cêwa an ɗauki wannan mataki tun yanzu domin samun sauƙi wajen tsara nunawan sabin ministoci a Majalisar Dattijai cikin shekara na 2017.

An yi rahoto cêwa wannan maye gurbi ya zama wajibi domin dakatar da ministoci wanda ba su yi aikin komai sai zaman banza, a yayin da shugaba Buhari yana fama da annoba na sukar wanda aka yi masa game da rashin aiki na Ministocinsa.

Domin tabbatar da cêwa an samu canji bayan zargin da aka yi masa, Shugaban Ƙasa Buhari ya shirya yin gyaran gwamnatinsa. Wannan wata shi ne na goma-sha-huɗu bayan an rantsar da Ministocin Buhari.

An bayyana cikin wannan rahoto cêwa za a cire waɗansu daga matsayin Minista, kuma za a canza mukami. Wannan canji ya zama wajibi domin har yanzu ba a cika gurbi na Ministoci guda biyu. Gurbin da za a cika shi ne na marigayi James Ocholi da Amina Mohammed. Maʼaikatan Shugaban Ƙasa basu ƙaryata wannan labari ba. Haka kuma basu tabbatar da gaskiyan wanan labari.

Punky

Cool Minded Blogger and Webmaster +2348022050583

Leave a Reply

Your email address will not be published.

%d bloggers like this: